Zanga-zangar kungiyar kwadago da sauran kungiyoyi akan rashin nuna kulawar da gwamnati tayi aka yajin aikin da ASUU keyi.

YAJIN AIKIN KUNGIYAR MALAMAN JAMI'OI NA KASA (ASUU), YAJAWO ZANGA-ZANGAR KUNGIYAR KWADAGO TA KASA (NLC), DAMA WASU KUNGIYOYIN YAU A ABUJA.
27 ga Yuli, 2022
ZANGA-ZANGAR KUNGIYAR KWADAGO
Saboda yajin aiki da kungiyar malaman jami'oi na kasa (ASUU) takeyi na tsawon lokaci kuma batare da gwamnati tayi wani abin kirki ba ko kuma wani kokari domin dakatar da hakan ba, haka yajawo cikashi akan harkokin ilimi a nigeria.

A ranar Laraba ne kungiyar kwadago ta Najeriya da kungiyoyin da ke goyon bayanta a Abuja suka cigaba da gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga yajin aikin watanni biyar da kungiyar malaman jami’o’i ta yi.

Shugaban NLC, Kwamared Ayuba Wabba, da dan takarar shugaban kasa na African Action Congress, Omoyele Sowore, da dai sauran su ne ke jagorantar zanga-zangar har zuwa ranar 2 ga watan Agusta mai zuwa a Abuja.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa kungiyoyin sun bijirewa gargadin da gwamnatin tarayya ta yi musu, inda suka fito kan titunan manyan biranen kasar a ranar Talata don nuna rashin amincewarsu da gazawar gwamnatin tarayya na warware yajin aikin na watanni biyar da kungiyar malaman jami'oi ASUU ta yi.

Musamman ma, kungiyar kwadago NLC ta ce kudaden da manyan jam’iyyun siyasa biyu – All Progressives Congress da Peoples Democratic Party – suke samu daga sayar da fom ga ‘yan takara za su iya magance bukatun na ASUU.

Malaman jami’o’in sun rufe cibiyoyin gwamnati ne a ranar 14 ga watan Fabrairu saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da ta kulla da ASUU a shekarar 2009 da kuma kin amincewa da gwamnati mai ci ta kebe malaman jami’o’in daga tsarin hada-hadar biyan albashi da na ma’aikata.

Kungiyar ASUU ta kuma bukaci gwamnati da ta kara yawan kudaden da ake baiwa manyan makarantu da kuma biyan wasu alawus alawus.

Amma a ranar Laraba, masu zanga-zangar sun taru a dandalin Unity Fountain, inda suka ci gaba da gudanar da zanga-zangar ta kwanaki biyu a Abuja, kan yajin aikin da ma’aikatan jami’o’in suke yi a fadin kasar.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan gudanar da irin wannan muzaharar a jihohi daban-daban na tarayyar kasar. 
Sai dai a babban birnin tarayya an fara zanga-zangar ne da misalin karfe 9:30 na safe bayan shugabannin kungiyar ta NLC da shugabannin kungiyoyi daban-daban, da kuma mambobin kungiyar sun hallara a dandalin Unity Fountain da ke babban birnin kasar.

Daga cikin wadanda suka halarci wurin akwai Wabba, Sowore, Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, da kuma tsohon shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, da dai sauransu.

Sai dai wakilan jaridar PUNCH sun bayyana cewa ta lura da yadda jami’an tsaro suka yi katsalandan a wurin zanga-zangar da suka hada da jami’an ‘yan sandan Najeriya, DSS, NSCDC da dai sauransu.

Wakilinmu ya tattaro cewa masu zanga-zangar sun shirya yin tattaki zuwa majalisar dokokin kasar inda shugaban NLC zai isar da sako daga kungiyoyin kwadago ga ‘yan majalisar.

Comments

Popular posts from this blog

RIKICI NA SHIRIN BALLEWA A JAMA'IYAR PDP.

WANNAN SHINE MAFI MUNIN CIN AMANA DA GWAMNATIN KASARNAN TAYIWA DCP ABBA KYARI.