MATSALAR TSARO A NIGERIA
Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Kwamared Shehu Sani, ya ce shugabannin tsaro a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba sa gudanar da ayyukansu. Tsohon dan majalisar ya yi magana ne a gidan talabijin na Arise TV kan tabarbarewar tsaro a kasar da kuma yadda ake ganin sakacin gwamnati na shawo kan lamarin. Ya ce, “Matsalar da muke fuskanta, ita ce kawai yadda shugabannin tsaro ba sa gudanar da ayyukansu. Majalisa ba za ta iya kore su ba. Shugaban kasa ne ya kamata ya dauki nauyi. Misali, a shekarar da ta gabata, ‘yan bindiga sun kai hari a makarantar horas da sojoji ta Najeriya, kuma an yi garkuwa da soja daya ko biyu. Ba a kori kowa ba. Babu wanda aka hukunta. Babu wanda ya yi murabus. Kuma alhakin shugaban kasa ne ya dauki mataki.” Ya ce majalisar dokokin kasar ta sha yin kira da a kori shugabannin jami’an tsaro ba tare da wata fa’ida ba. “Sau da yawa a lokacin da muke majalisar dokokin kasar, mun yi kira da a kori shugabannin tsaro. Sai dai hoton da ake ta...