An gano dimbin yaran da aka yi garkuwa da su a gidan karkashin kasa na wata coci a Ondo.

An gano dimbin yaran da aka yi garkuwa da su a gidan karkashin kasa na wata coci a Ondo.
Yuli 5, 2022.

An yi zargin cewa an gano kananan yara da dama a wani gida na karkashin kasa na wani coci da ke Unguwar Valentino da ke garin Ondo a Jihar Ondo a yammacin ranar Juma’a.

An tattaro cewa ana zargin an yi garkuwa da yaran ne aka ajiye su a wani dakin karkashin kasa na cocin.

Wata majiya ta ce wadanda abin ya shafa sun haura 50 yayin da ‘yan sanda suka kubutar da su tare da kame limamin cocin da wasu ’yan cocin.

A cikin wani faifan bidiyo, an ga yaran a cikin wata motar sintiri na ‘yan sandan da ta kai su ofishin ‘yan sanda.

A cikin hoton bidiyo na dakika 1 da dakika 40, an ji wata murya tana cewa, “Yaran da aka yi garkuwa da su ne da aka gano a dakin da ke karkashin kasa na wani coci a Unguwar Valentino a Ondo. An kama limamin cocin da wasu ’yan cocin kuma suna cikin motar ‘yan sanda da ke sintiri.

Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mrs Funmilayo Odunlami, ta ce an kai wadanda harin ya rutsa da su hedikwatar rundunar ta Akure.

“Bani da cikakken bayani tukuna amma suna kawo wadanda abin ya shafa hedikwatar. Zan ba ku cikakken bayani da zarar na samu daga DPO,” in ji PPRO.

Comments

Popular posts from this blog

RIKICI NA SHIRIN BALLEWA A JAMA'IYAR PDP.

Zanga-zangar kungiyar kwadago da sauran kungiyoyi akan rashin nuna kulawar da gwamnati tayi aka yajin aikin da ASUU keyi.

WANNAN SHINE MAFI MUNIN CIN AMANA DA GWAMNATIN KASARNAN TAYIWA DCP ABBA KYARI.