Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Alhamis 1 ga watan Zul Hijjah, Asabar Eidul Adha
Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Alhamis 1 ga watan Zul Hijjah, Asabar Eidul Adha
Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya sanar da ranar Alhamis 30 ga...
Mai Martaba Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar III.
By
Mahanga Hausa news
Laraba, 29 ga Yuni 2022 21:28:16 GMT
Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Alhamis 30 ga watan Yuni a matsayin Dhul Hijjah 1, 1443AH.
Wannan yana nufin ranar Asabar 9 ga watan Yuli ita ce ranar Eidul Adha ko kuma ranar sallah, tana zuwa bayan Juma'a 8 ga Yuli, wato ranar Arafat.
A wata sanarwa da kwamitin ganin wata na kasa (NMSC) ya fitar, ya ce Sultan Abubakar ya ayyana ranar Alhamis 30 ga watan Yuni a matsayin ranar daya ga watan Dhul Hijjah.
"Eidul Adha zai kasance ranar Asabar 10th Dhul Hijjah 1443H (9 ga Yuli 2022) In Sha Allah.
“Mai martaba Sarkin Musulmi yana kira ga al’ummar musulmi da su kara himma wajen gudanar da ibada a cikin kwanaki 10 na farkon watan Dhul Hijjah mai albarka.
"Sannan kuma a yi addu'ar zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban kasa," in ji sanarwar.
Comments
Post a Comment